✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LP ta lashe zaben dan Majalisar Tarayya na Jos da Bassa

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Daniel Asama na Jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin dan Majalisar Tarayya na Mazabar…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Daniel Asama na Jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbin dan Majalisar Tarayya na Mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato, wanda aka gudanar ranar Asabar.

Babban jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa James Garba, ya sanar da cewa Daniel Asama ya lashe zaben da kuri’u 66,422.

Ya sanar kuma cewa ɗan takarar Jam’iyyar PRR, Gwani Adam Alkali ya sami kuri’u 61,670 sai Hassan Baba na APC da ya sami kuri’u 10,063.

A yanzu Daniel Asama zai maye gurbin dan majalisar wannan mazaba, Musa Agah na Jam’iyyar PDP, wanda kotun daukaka kara ta rushe zaɓensa, saboda kasa cika ka’idojin shiga zaben da ya gabata, kuma ta umarci a sake zaben.