✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Dalibai sun yi bore kan albashin malamai na wata 10 a Taraba

Daliban dai sun rika kona tayoyi tare da rufe wasu hanyoyin Jalingo

Daruruwan daliban Jami’ar Jihar Taraba da ke garin Jalingo sun yi zanga-zanga kan rashin biyan malamansu albashin wata 10.

Daliban sun rika kona tayoyi tare da lalata dukkan wata alama ta Jam’iyar PDP da ke mulkin jihar a garin Jalingo, babban birnin jihar.

’Yan sanda dauke da bindigogi ne aka tura a sassa birnin da kuma gidan gwamnatin Jihar inda masu boren suka yi kokarin kutsawa amma jami’an tsaron suka hana su.

’Yan sandan suka rika yin harbi a sama kafin su watsa daliban daga hanyar da ta shiga gidan gwamnati.

Su ma sojoji sun shiga aikin kwantar ta tarzomar zanga-zangar, inda  suka lakada wa wasu daga cikin daliban duka.

Har zuwa lokacin hada wannan labarin dai kura ba ta lafa ba, kuma wasu daga cikin hanyoyin garin ba sa biyuwa saboda tsoron masu zanga-zangar ko kuma gudun fadawa hannun jami’an tsaro.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewa an tura jami’ansu masu yawa domin kwantar da tarzoma.