✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibar jami’a ta rasu bayan fadawa sokawen makaranta

Masu aikin ceto sun kai ta asibitin koyarwar jami'ar, amma rai ya yi halinsa

Wata daliba ’yar aji biyu a jami’a ta rasu bayan ta fada a cikin sokawen dakunan kwanan dalibai a Jami’ar Obafemi Awolowo ta Ile-Ife.

Dalibar mai suna Ajibola Heritage Ayomikun ta gamu da ajalinta ne bayan ta fada a cikin sokawen dakunan kwanan dalibai masu zaman kansu a jami’ar.

Faduwar Ajibola, wadda ke karatu a banfaren Fasahar Harsuna, ke da wuya, aka kira ma’aikatan hukumar kashe gobara suka kawo dauki, suke ciro ta.

Nan take suka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo, amma rai ya riga ya yi halinsa.

A yayin da jagoranci hukumar gudanarwar jami’ar suka kai wa iyayen dalibar ziyarar ta’aziyya, Shugaban jami’ar, Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya bayyana damuwa game da rasuwar dalibar.

Farfesa Eyitope, ya ce za a gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa faduwar dalibar a cikin sokawen da ya yi adalin dalibar tare da hukunta duk wadanda aka samu da laifi.

Sannan ya bukaci dalibai da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na neman ilimi yadda ya kamata.

Farfesa Eyitope, ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Abiodun Olarewaju, ya bayyana takaicinsa a kan abin da ya faru, wanda ya ce jami’ar ba za ta bari ya tafi haka nan ba.

Ya ce an sanar da hukumar ’yan sanda kuma sun fara gudanar da bincike kan abin da ya faru.