✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilina na yin watsi da shawarar zuwa Landan duba lafiyata —Aisha Buhari

Sai da raina ya baci saboda shawarar da aka bani a kan tafiya Landan ganin Likita.

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayyana abin da ya sa a wani lokaci na rashin lafiya ta yanke shawarar zuwa duba lafiyarta a wani asibitin kudi a nan gida Najeriya a maimakon tafiya Landan kamar yadda maigidanta ya saba.

Aisha ta bayyana hakan ne a cikin sabon littafin rayuwarta da aka kaddamar ranar Alhamis, wanda a cikinsa ne kuma ta bayyana mummunan halin da Asibitin Fadar Gwamnatin Najeriya ya taba tsintar kansa a ciki saboda rashin ingatattun kayan aiki.

A cewarta, “akwai wani lokaci da raina ya baci saboda shawarar da aka ba ni a kan tafiya Landan ganin likita yayin da nake rashin lafiya.

“Na tsinci kaina cikin takaicin yadda a wani lokaci Asibitin Fadar Aso Rock ya kasance ba ya aikin da ya dace na kula da iyalan Shugaban Kasa da sauran ma’aikatan fadar a lokacin rashin lafiya.

“A kan haka ne a wancan lokaci na yi Allah-wadai da masu kula da asibitin da kuma yadda ake gudanar da shi saboda yadda bai wadata da ingatattun kayan aikin duba marasa lafiya ba.

“Hakan ya sanya na ziyarci wani asibitin kudi bayan na gano cewa injin daukar hoton cikin jikin mutum da ke Asibitin Fadar ba ya aiki ko kadan,” a cewar Aisha.

Ana iya tuna cewa furucin da Aisha Buhari ta yi a ranar 9 ga watan Oktoban 2017 yayin wani taron masu ruwa da tsaki a kan kiwon lafiyar mata da kananan yara ya janyo cece-kuce, inda ta yi magana kan muhimmancin inganta harkokin kiwon lafiya a kasar.

Aisha ta yi kaurin suna wajen gargadin masu rike da madafan iko a kasar nan kan siyasantar da lamarin da ya shafi harkokin kiwon lafiya da kuma tallafa wa mata.

Aminiya ta ruwaito cewa, Dokta Hajo Sani, babbar mai taimaka wa Shugaban Kasa ta musamman kan harkokin mata, ce ta rubuta littafin wanda aka kaddamar a wani kasaitaccen biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja.

An kaddamar da littafin mai suna, “Aisha Buhari: Being Different” ma’ana “Aisha Buhari: Yadda ta Bambanta”, a daidai lokacin da Shugaba Buhari ke ganin likitocinsa a Landan.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya wakilci shugaban kasar yayin bikin.