✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin haramta sinadaran karin dandano a Kano

An fara kama masu sayar da kayan kara armashin kayan shaye-shaye da dangoginsu.

Gwamnatin Jihar Kano ta haramta amfani da sinadaren karin dandano, ko armashi ko tsamin lemo saboda zargin su da haddasa barkewar cuta a Jihar.

Gwamnatin Kano ta dauki matakin ne bayan barkewar wata annoba da ta kwantar da sama da mutun 160 a sassan jihar, da ake zargi na da nasaba da amfani da kayan shaye-shaye.

Tuni dai aka baza jami’ai domin kama masu sana’ar sayar da kayan da suka hada da ‘Dan tsami da Flavour da Citric Acid da dangoginsu’, tana kuma rokon jama’a da su falla masu yin ta da suka ki dainawa.

Ta ce an yi haka ne bayan gwajin da ta gudanar kan mutanen da ke kwance a asibitoci sakamakon rashin lafiya da suka kamu da ita bayan amfani da kayan lemon a sassan jihar.

Shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu Siyayya ta Jihar,  Bafffa Babba Dan Agundi, ya ce wa’adin yawancin sinadaran na ‘Dan tsami da Flavour da Citric Acid’, da ake hada kayan shaye-shayen da su ya kare.

Ya kuma ce hukumar ta kama buhu 583 na gurbatattun sinadaran da dangoginsu a wani kamfani da ya yi kaurin suna wajen sayar da irinsu da aikinsu ya kare a Karamar Hukumar Minjibir ta Jihar.

Kungiyar masu sana’ar kayan sinadaren kara armashin kayan shaye-shaye a Jihar ta nesa kanta da matsalar, tana mai cewa bata-garin cikinsu ne ke bata musu suna.

Shugaban Kungiyar, reshen Jihar, Abubakar Isah Muhammad, ya ce kungiyar ta kaddamar da yaki da miyagun cikinsu