Dan majalisar Gombe ya sauya sheka daga APC zuwa PDP | Aminiya

Dan majalisar Gombe ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

PDP da APC
PDP da APC
    Rabilu Abubakar, Gombe

Dan Majalisar Wakiltai daga mazabar Gombe da Kwami da Funakaye a Jihar Gombe, Yaya Bauchi Tongo, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Dan majalisar dai ya fita ne tare da dimbin magoya bayansa da ya ce yawansu ya kai kimanin 11,000 daga Karamar Hukumar Funakaye ta jihar Gombe.

 

A cikin wata wasikar da dan majalisar ya aike wa jam’iyyarsa a watan Disamban 2021, ya ce rikicin cikin gidan da ya dabaibaye jam’iyyar ne yasa ya fice daga cikinta.

Hon. Yaya Bauchi Tongo

Hon. Yaya Bauchi Tongo rike da sabon katinsa na PDP

 

Ya kuma kalubalanci shugabanin jam’iyyar kan yadda suke nuna wariya ga ’ya’yanta ciki har da shi musamman a zaben shugabanin jam’iyyar da ya gudana.

A cewarsa, “Hukuncin da na yanke na barin jam’iyyar ya biyo bayan rikice-rikicen cikin gidan da ya dabaibaye jam’iyyar ne kuma ba a iya magance shi ba.”

“Duk wani kokari da mambobin jam’iyyar ta APC suka yi wajen ganin an
sasanta ya gagara sai ma kara samun matsaloli ake yi, inda yanzu haka
an kwace mana damar, wasu ’yan kalilan ne suke juya akalar jam’iyyar,
an ki a ba mu dama mu ba da gudumawarmu don ciyar da ita gaba,” inji shi.

A wani labarin kuma, ’ya’yan jam’iyyar kusan 11,000 ne suka sauya shekar daga APC suka koma PDP a Karamar Hukumar ta Funakaye tare da shi dan majalisar.

Sai dai ko da wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC, Moses Kyari, kan canja shekar, ya ce sun bar jam’iyyar ne kawai don bukatar kashin kansu saboda ganin ba za su sake samun tikitin takara a zaben 2023 ba.