✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Wakilai daga Sakkwato ya rasu

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Isa-Sabon Birni daga Jihar Sakkwato, Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu.

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Isa-Sabon Birni daga Jihar Sakkwato, Honorabul Abdulkadir Jelani Danbuga ya rasu. 

Dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Aminu Almustapha (Boza) ya  shaida wa wakilinmu cewa Honorabul Abdulkadir Jelani Danbuga ya saru ne bayan gajeriyar rashin lafia.

Ya ce da farko an kwantar da marigayin a asibiti a ranar Talata, kafin Allah Ya yi masa cikawa da misalin 12.30 na dare.

Ya ce, “Za a kai shi Babban Masallacin Kasa da ke Abuja, inda za a yi masa wanka, sannan a kai shi Sakkwato a yi masa Sallar Janaza,” in ji shi.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya da kuma jikoki.