Dan majalisarsu Kwankwaso ya fice daga NNPP zuwa APC | Aminiya

Dan majalisarsu Kwankwaso ya fice daga NNPP zuwa APC

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano
    Sagir Kano Saleh da Zahraddeen Yakubu Shuaibu, Kano 

Dan Majalisa mai wakilatar mazabar tsohon Gwamna Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya sauya sheka daga NNPP zuwa APC.

Dan Majalisa Hon. Kabiru Yusuf Isma’il, mai wakiltar Madobi, mazabar Kwankwaso, a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya sauya sheka zuwa APC ne kwana kadan bayan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya suaya sheka daga APC zuwa NNPP.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar ta ce shi ma dan majalisar dokokin da ke wakiltar Dawakin Kudu, Mu’azzam El-Yakubu, ya fice daga jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP ya dawo APC.

A cewarsa, ’yan majalisar dokokin Jihar da ta Kasa da dama na ta sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin jihar.

Daga cikin masu sauya shekar har da dan majalisa mai wakiltar  Bagwai/Shanono, Isa Ali, wanda ya baro NNPP ya dawo APC.

A baya-bayan nan dai, ’yan siyasa na ta sauya sheka a Jihar Kano, a yayin da babban zaben 2023 yake kara matsowa.

A watan Afrilu, ’yan majalisar dokokin jihar 14 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar APC da PDP zuwa NNPP.

Sai kuma, kwanaki kadan bayan haka kuma wasu daga cikinsu suka sake dawowa APC.