✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar PDP ne ya lashe zaben cike gurbi a Kaduna – INEC

INEC dai ta shirya zaben ne biyo bayan ayyana kujerar a matsayin wacce babu kowa a kai.

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Hon. Usman Ali-Baba a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi a mazabar dan Majalisar Jiha mai wakiltar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Baturen zabe na yankin, Dokta Muhammadu Nuruddeen Musa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ne ya bayyana zaben da safiyar ranar Lahadi.

A cewarsa, dan takarar ya sami kuri’a 9,113, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na jam’aiyyar APC, Musa Ahmed Musa, wanda ya sami kuri’a 7,404.

INEC dai ta shirya zaben ne na ranar Asabar biyo bayan ayyana kujerar wanda ke kai a matsayin wacce babu kowa, bayan wakilin mazabar, Hon. Aminu Shagali ya ki halartar kashi daya bisa uku na zaman majalisar.

Shagali dai shine ya sauka daga Shugabancin majalisar kafin shugabanta na yanzu ya hau kai, kuma ya wakilci mazabar ne tun shekarar 2011.

A watan Afrilun bana, Shagali ya yi fatali da matakin da majalisar ta dauka na ayyana kujerarsa a matsayin wacce babu kowa a kai, har ma ya yi barazanar daukar matakin shari’a.

Sai dai zaben na ranar Asabar ya fuskanci karancin fitowar masu kada kuri’a matuka a mazabun Muchia da Chikaji da Jushin Waje da Unguwan Gabas da Zabi da kuma Hanwa na Karamar Hukumar ta Sabon Gari.

Sauran jam’iyyun da suka fafata a zaben sun hada da PRP da ADC da kuma ADP.