✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote ya koma matsayi na 129 a jerin attajiran duniya — Forbes

Amurka ta fi kowace kasa yawan attajirai inda ta mamaye jerin da manyan attajirai 813.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya kare kambinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyyar Afirka.

Wannan dai na kunshe ne cikin sabbin alkaluman da Mujallar Forbes ta Amurka wadda ta mai da hankali kan kididdige harkokin kasuwanci, hannun jari, fasaha, jagoranci da salon rayuwa ta fitar a makon nan.

Dangote wanda fitaccen dan kasuwa ne na cikin sahun wasu hamshaƙan attajirai na Najeriya da suka shiga cikin jerin manyan attajiran duniya na shekarar 2024 kamar yadda Mujallar Forbes ta wallafa.

A cewar Forbes, Dangote ya shi ne mutumin da ke matsayi na 129 a cikin jerin attajiran duniya yayin da dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 15.0, lamarin da ya tabbatar da matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.

Sauran fitattun ’yan kasuwar Najeriya da suka shiga cikin jerin attajiran duniya sun hada Mike Adenuga, shugaban kamfanin Globacom, da ya zo na 407 da arzikin da ya kai dalar Amurka  biliyan 6.9.

Akwai kuma Abdulsamad Rabiu, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA da ke matsayi na 462 da dukiyar da ta kai dalar Amurka biliyan 6.3, sai kuma Femi Otedola da ke sahu na 1906 a cikin jerin attajiran wanda dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 1.7.

Mujallar Forbes dai ta fitar da kididdigar ce ta hanyar amfani lissafin farashin hannun jari da farashin musayar kudi tun daga Maris 8, 2024.

Amurka ce ta mamaye jerin da manyan attajirai 813, inda lissafin dukiyarsu ya kai dala tiriliyan 5.7.

China ta biyo bayanta da attajirai 473 da darajarsu ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.7, yayin da Indiya ta samu matsayi na uku da attajirai 200.

Alkaluman kudin attajirai na duniya a bana ya kai dala tiriliyan 14.2 wanda ba a taɓa ganin irinsa ba, wanda ya nuna ƙaruwar dala tiriliyan 2 na alkaluman shekarar da ta gabata.

Waɗannan alƙaluma sun nuna irin ɗimbin arziki da tasirin da manyan ƙasashen duniya ke da shi, da kuma yadda tattalin arzikin duniya ke ci gaba da bunƙasa da kasuwanci.