✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Daso ta samu mabiya miliyan 1 a Instagram

Fitacciyar jarumar ta ce tana fatar ganin mabiyanta sun kai miliyan 100.

Fitacciyar jarumar masana’antar fim ta Kannywood, Saratu Gidado, wadda aka fi sani da Daso ko Mama Daso ta kai matakin mabiya miliyan a Instagram.

Domin murnar kaiwa wannan matakin, Daso ta wallafa a shafinta cewa, “Ina kara godiya ga masoyana fa. Ba don ku ba da ban kai haka ba. Allah Ya saka muku da alheri. Ina son ku kara yawa ku zama miliyan 1000 insha Allah.”

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Saratu Gidado Daso (@saratudaso)

Instagram kafa ce da aka fi sanin matasa da shiga, sun kuma fi tara mabiya da yawa a kafar wadda ba kasafai ake samun dattawan Kannywood da ke shigar ta ba.

Ko a cikin matasan matan, ba dukansu ba ne yawan mabiyansu ya akai miliyan daya, wanda hakan ya sa Daso ta ciri tuta.