✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattawan Arewa sun bukaci Buhari ya yi murabus saboda matsalar tsaro

’Yan ta’adda sun hana mu sakat, sun hana mu ’yancinmu na yin rayuwa cikin aminci da tsaro.

Kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF), ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus a sakamakon yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara musamman a Arewacin kasar.

Mai magana da yawun kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ne ya yi wannan kira a ranar Talata.

Dokta Hakeem ya ce Buhari bai da wani zabi illa kawai ya yi murabus ganin yadda ya gaza sauke amanar da ya dauka musamman a halin da kasar ta sami kanta a halin yanzu na balbalcewar tsaro.

“A bayyane take karara cewa gwamnatin Shugaba Buhari ba ta da wani tsimi ballantana dabarun tunkarar kalubalen tsaro da ya addabi kasar nan.

“Ba zai yiwu mu ci gaba da zama ana kashe mu. A halin da muke ciki masu garkuwa da mutane, fyade da sauran masu tayar da zaune tsaye da gungun ’yan ta’adda sun hana mu sakat, sun hana mu ’yancinmu na yin rayuwa cikin aminci da tsaro.

“Kundin tsari mulkin Najeeriya ya yi tanadin cewa shugabannin su yi murabus a duk sa’ilin da suke fuskantar wasu kalubalen da ba za su iya magance su ba.

Ana iya tuna cewa ko a shekarar 2020, kungiyar Dattawan Arewan ta bukaci Buhari da ya sauka daga mulki a sakamaon yadda matsalar tsaron kasar ta tabarbare.