✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dattawan Arewa sun soki Tinubu kan ƙara kuɗin wutar lantarki

Ƙungiyar ta ce ƙarin kuɗin bai dace da yanayin da al'ummar ƙasar nan ke ciki ba.

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta nuna rashin jin dadinta kan matakin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka na kara kuɗin wutar lantarki.

Ƙungiyar ta bayyana ƙarin a matsayin rashin dacewa da kuma mutunta walwala da jin daɗin al’ummar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran kungiyar, Abdul-Azeez Suleiman ya fitar, ƙungiyar ta ce ƙarin zai haifar mummunan tasiri ga tattalin arziƙin al’ummar ƙasar nan.

“Sabon tsarin biyan kuɗin wutar lantarki na sa’o’i 24 a kowace rana zai tashi daga Naira 5,400 zuwa Naira 162,000, wanda kuma a shekara kuɗin zai iya kamawa Naira 1,971,000.

“Waɗannan makuɗan kuɗaɗe ‘yan Najeriya ba za su iya biya ba, saboda mutane na fama da matsalar tattalin arziki da kuma ƙoƙarin samun abun biyan buƙata.

“Bijiro da ire-iren waɗannan tsare-tsare da gwamnati ke yi ba abin da zai haifar face sake jefa ƙasar nan cikin matsi.

“Ya kamata a yi shawara kafin aiwatar da irin wannan ƙari, duba da irin tasirin tabarbarewar tattalin arziki ya yi ga ‘yan ƙasa.”

Ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da ‘yan Najeriya za su tashi domin bin ba’asin yadda shugabanni ke mulkar su.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki (NERC), ya sanar da ƙarin kuɗin wutar lantarki.

Sai dai kamfanin ya ce ƙarin zai shafi rukunin mutanen da ke samun wutar aƙalla sa’o’i 24 a rana ne kaɗai.