✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Titin Legas-Kalaba: Duk kilomita 1 za ta laƙume 4bn — Minista

Ministan ya ce za a shafe shekara takwas ana aikin kafin ya kammala.

Ministan Ayyuka na Kasa, David Umahi, ya ce duk kilomita ɗaya na aikin hanyar gabar ruwan Legas zuwa Kalaba da ake yi zai laƙume Naira biliyan huɗu. 

Ya bayyana haka ne a wani martani da ya yi wa Atiku Abubakar, kan cewar aikin kowace kilomita na titin na laƙume Naira biliyan takwas.

Umahi, ya ce aikin hanyar ya kai kimanin kilomita 700 wanda aƙalla zai laƙume Naira tiriliyan 2.8.

Ministan, ya yi wannan warwara ne yayin tattaunawarsa da Gidan talabijin TVC.

Ya musanta zargin da ake yi na cewa ba abi ƙa’idojin da suka dace ba wajen bayar da aikin.

A makon da ya gabata ne, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku ya soki matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka na bayar da kwangilar aikin ga kamfanin Gilbert Chagoury’s Hitech ba.

Atiku ya yi zargin cewar ba a bai wa wasu ’yan kwangila dama domin su gabatar da buƙatarsu a tantance ba.

Atiku, ya yi ikirarin cewa har yanzu shugaba Tinubu ya gaza bayyana cikakken kuɗin da za a kashe a aikin hanyar Legas zuwa Kalaba.

Sannan ya ce ya yi mamakin yadda Tinubu ya  biya Naira tiriliyan 1.5, na aikin Eko Atlantic wanda zai dire a tashar ruwa ta Lekki Deep Sea Port.

Sai dai Umahi, ya bayyana tsadar kayan gine-gine da hauhawar farashi a matsayin abin da ya sa aikin zai laƙume kuɗi da yawa.

Ya bayar da tabbacin aikin zai kammala cikin shekara takwas.