✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dimokuradiyyar da babu dimokuradiyya a cikinta

A ra'ayin Aminiya, dauki-dora da suna maslaha karan-tsaye ne ga dimokuradiyya

Badi iyanzu za a yi rubu’in karni tun bayan samuwar tsarin dimokuradiyyar da ake aiwatarwa yanzu a Najeriya — wanda shi ne mafi dadewa a tarihin kasar nan.

Wannan tsawon lokaci ya yi daidai da shekarun da sojoji suka kwashe — 29 — suna mulki.

Wannan kwatance yana da muhimmanci saboda wasu dalilai wadanda suka hada da zargin sojojin da aka yi — babu kage a hakan kuma — da kafa haramtacciyar gwamnati, da almundahana, da kuma dakile ci gaban kasa.

Amma kuma, za a iya cewa tsarin dimokuradiyya ya kawo sauyi a kowanne daga cikin wadannan abubuwa? Zai yi wuya.

Martabar zabubbuka

Tun bayan dawowar mulkin farar hula, an samu wasu muhimman nasarori biyu: sauyin gwamnati — ma’ana mika mulki daga zababben shugaban kasa zuwa wani zababben — cikin lumana a 2007 da kuma mika mulki ga ‘yan adawa a 2015.

Sannan kuma martabar zabubbukanmu ta karu sosai, musamman a manyan zabubbuka uku da suka gabata.

Sai dai kuma, baya ga wannan, ingancin dimokuradiyyar Najeriya sai raguwa yake yi — alamar mummunan ci bayan da ake samu a fadin Afirka inda ake ta samun dawowar juyin mulki a kasashe da dama.

Kuma ba kowa ne yake kawo wannan nakasu ba illa jam’iyyun siyasar Najeriya da ‘yan siyasar da suke tafiyar da su.

Koma-baya

A watan Oktoba na bara babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi wani babban taron kasa don zaben sababbin shugabanni, bayan an yi tarurruka a jihohi da kananan hukumomi.

Ranar Asabar kuma jam’iyyar APC mai mulki ta yi nata taron bayan an shafe watanni ana ta rikicin cikin gida da na shugabanci wadanda ba a kai ga warware su ba gaba daya.

A tarurrukan biyu dai daga waje akwai kamshin dimokuradiyya, amma idan aka leka ciki za a ga babu ita ko kusa ko alama.

Tsarin maslaha wajen zaben shugabanni, ko da yake abu ne karbabbe a dimokuradiyya, ya zama wani babban makami a jam’iyyun biyu na dakushe dimokuradiyyar.

Wannan tsarin na maslaha, a yadda APC da PDP suke amfani da shi, yana kuntata fagen dimokuradiyya ba kawai ga ‘yan jam’iyya ba har ma ga al’ummar kasa masu kada kuri’a.

Galibi wasu fulogan jam’iyya ‘yan kalilan ne ke zabo wanda zai yi takarar mukamin jam’iyya ko na gwamnati, ba tare da tuntuba ko musayar ra’ayin da ake bukata a tsarin maslaha ba.

Mummunan sabani

Wannan ne yake haifar da gagarumin sabani a tsakanin ‘yan jam’iyya da kararraki a kotu bayan tarurrukan.

Idan ‘yan jam’iyya ba su da ikon zaben shugabanninsu ko wadanda za su yi takarar mukaman gwamnati, to asarorin da ake tafkawa za su hadu su yi katutu su zaizaye sahihancin dimokuradiyyar a kasa.

Hakan kuma kan haramta wa jam’iyyun siyasa da ma kasa baki daya damar samar da sababbin shugabanni masu sabon tunani da sabuwar mahangar da za su taimaka a dora jam’iyyar ko kasar a turba mafi inganci.

Hakan yakan hana muhawarar da za ta taimaka wajen ilmantar da masu zabe game da akida ko manufar siyasa.

Yakan kuma takaita shigar al’umma a dama da ita ta hanyar gabatar wa masu zabe zabin ‘yan takara da manufofin da, a zahiri, ba zabi ba ne sam.

Danjuma da Danjummai

Wannan ne yake sanyawa a samu jam’iyyun siyasar da ba su da wani bambanci na a zo a gani da juna saboda babu wadda ta gabatar da wani abu, ko wani mutum da zai aiwatar da wani abu, mai kama da burace-buracen ‘yan Najeriya.

Wadannan abubuwa ne kuma suke kara tsanantar rashin fita domin kada kuri’a, al’amarin da ka iya haifar da rashin halalci ga gwamnatoci ya kuma rage kwarin gwiwar mutane game da tsarin dimokuradiyya.

A wannan mahangar sai zabe — a matakin jam’iyya ko wanda ya shafi al’umma baki daya — ya zama wani matakin je-ka-na-yi-ka na yin fentin halalci wa wadansu mutane da aka nada wadanda watakila ma ba su cancanta ba, a maimakon wata sahihiyar hanya ta raba tsaki da tsakuwa.

A yau ba sai gobe ba, dimokuradiyyar Najeriya a wannan mataki take.

Yayin da kashi 52 cikin 100 na mutum kusan miliyan 58 da suka yi rajista ne suka kada kuri’a a zaben shugaban kasa na 1999, kashi 33 cikin 100 ne kacal suka yi zabe shekara 20 bayan nan a zaben shugaban kasa na 2019 duk da yawan wadanda suka yi rajista ya karu zuwa sama da miliyan 82, kudin da aka kashe don gudanar da zabe kuma ya kai daruruwan biliyoyin Naira.

Ga shi kuma babu wasu kwararan alamu da suke nuna za a samu wani sauyi a 2023.

Dauki-dora

Duk da cewa mun shiga shekarar zabe, ba a gudanar da zabubbuka saboda manyan jam’iyyun kasar nan biyu sun zabi su yi nadin ‘yan takara ta hanyar maslaha a maimakon baje komai a faifai don bai wa kowa damar gwada farin jininsa.

Bayan ta yanke shawara a kan shugabanninta ta hanyar maslaha, a yanzu haka jam’iyyar adawa ta PDP ta dukunkune a kuntatacciyar siyasar dauki-dora a yunkurin samar da dan takarar shugaban kasa da ‘yan takarar gwamna.

Akwai yiwuwar ita ma jam’iyyar APC mai mulki za ta bi sahu a yayin zaben fitar da gwani.

Sam wannan ba zai yi kyau ba ga makomar dimokuradiyyar Najeriya sannan ya yi hannun riga da abin da ya faru a Jamhuriya ta Biyu, lokacin da aka bai wa kowa dama ya gwada kwanjinsa.

Mu a Aminiya ba makauniyar adawa muke yi da takarar maslaha ba.

Babbar damuwarmu ita ce yadda manyan jam’iyyun kasar nan suke yin ta a yanzu ta hanyar da ta yi karan-tsaye ga dimokuradiyya da rashin tuntubar juna.

Maslahar da ba maslaha

Duk yanayin da zai sa shugaban kasa da gwamnoni — a daidaikunsu ko a kungiyance — da wasu shugabannin jam’iyya kalilan za su kwashi wasu ‘yan takara su kakaba wa jam’iyyu da ma ‘yan Najeriya da sunan “maslaha”, to ba kawai saba wa dimokuradiyya ya yi ba, almundahana ne.

Shi ne kyakkyawan misalin amfani da mukami ta hanyar da ba ta dace ba da yin karfa-karfa.

Wadannan ne muke adawa da su, babu gudu ba ja da baya.

Yayin da muke shiga kakar zabubbukan fitar da gwani ka’in da na’in, muna kira ga jam’iyyun siyasar kasar nan musamman PDP da APC, su kyale kowa ya shigo fili ya gwada farin jininsa — ko dai ta hanyar bai wa daukacin ‘yan jam’iyya dama ko ta hanyar amfani da daliget-daliget.

Za su yi hakan ne ba don maslaha ba halaltacciyar hanyar fitar da ‘yan takara ba ce, sai don wani lokaci akan bar halal don kunya.

Kimar ‘yan Najeriya ta wuce maslahar da babu maslaha.