✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diyyar jinin Sheikh Goni na wuyan Rundunar Sojin Najeriya —Bukarti

Bukarti ya ce dole rundunar soji ta biya diyya ga iyalan malamin, saboda da makaminta aka yi amfani kuma sakacinta ne abin ya faru

Fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare hakkin bil Adama, Bulama Bukarti, ya dora alhakin kisan Sheikh Goni Aisami kan Rundunar Sojojin Najeriya.

Lauyan ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda yake bayyana alhininsa kan kisan shehin malamin da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Bukarti ya dora alhakkin kisan Sheikh Goni Aisami kacokam a kan Rundunar Sojin Najeriya, yana mai kafa hujja da cewa wanda ya aikata kisan, John Gabriel, soja ne, kuma da bindigarsa ta aiki ya yi hakan.

Bulama ya ce, “Akwai sakacin Rundunar Sojin Najeriya dangane da aikata laifin kisan.

“Dole rundunar sojin ta biya diyya ga iyalan mamacin domin da rigarsu da makaminsu wannan dan fashi ya yi amfani kuma sakacinsu ne,” in ji Bulama Bukarti.

Bulama ya yi kira da a gaggauta hukunta wanda ya aikata kisan, wato John Gabriel, tare da wanda ya taimaka masa.