✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dokar Cire Kudi: Emefiele ba zai bayyana gaban Majalisa ba

Gwamnan CBN ya kafa kwamitin da zai wakilce shi wajen amsa gayyatar Majalisar.

Gwamnan Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya rubuta wa Majalisar Wakilai wasika don sanar da ita dalilan da za su hana shi amsa gayyatarta da kansa.

Wasikar da Shugaban Majlisar, Femi Gbajabiamila ya karanto a zauren majaisar a zamanta na ranar Laraba, ta nuna Emefiele yana kasar waje ne domin duba lafiyarsa.

Gbajabiamila ya ce, Gwamnan CBN ya bayyana a cikin wasikar tasa cewa ya kafa kwamitin da zai wakilce shi wajen amsa gayyatar a saboda muhimmancinta.

A ranar Alhamis ake sa ran Emefiele ya bayyana a Majalisar, sai dai a halin da ake ciki yana kasar  Amurka.

Hakan ya sa ya rubuta wa Majalisar wasika yana mai nuna rashin jin dadinsa kan rashin samun damar amsa gayyatar da kansa.

Yanzu dai kwamitin da Gwamnan CBN din ya nada karkashin jagorancin Aisha Ahmed, ake sa ran ya bayyana a gaban Majalisar don yi mata bayani a madadinsa.