✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana acaba: Gwamnatin Legas ta ragargaza babura 2,000

Gwamnati ta ce ta yi hakan ne don ta nuna dokar na nan daram

Gwamnatin Jihar Legas ta ragargaza babura guda 2,000 da ta kwace daga hannun ’yan acaba bayan dokar hana sana’ar a da ta saka a wasu Kananan Hukumomin Jihar ta fara aiki.

Gwamntin dai ta haramta sana’ar ne a wasu Kananan Hukumomi da Gundomomin Raya Kasa guda shida da ke Jihar, kuma dokar ta fara aiki ne daga farkon watan Yunin 2022.

Kwamishinan Sufuri na Jihar, Dokta Frederic Oladeinde, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a birnin Legas.

Ya bs da tabbacin cewa matakin da gwamnatin ta dauka na hana sana’ar a yankunan don kare rayuka da dukiyoyin al’umma na nan ba gudu ba ja da baya.

Shi ma da yake yi wa manema labarai jawabi lokacin da ake ragargaza baburan a unguwar Ikeja, Kwamishinan Yada Labarai da Tsare-tsare na Jihar, Gbenga Omotosho, ya ce sun dauki matakin ne don su nuna cewa gwamnati ba da wasa take ba.

Kwamishinan, wanda ya kuma jinjina wa al’ummar Jihar saboda yadda suka bi dokar, ya kuma ce ya zuwa yanzu, an gurfanar da mutum 21 a gaban kotu, sannan an kwace babura 2,000.

Gbenga ya kuma ce gwamnati ta yi tanadi ga ’yan acabar da haramcin ya shafa na motocin bas-bas domin su ci gaba da samun abin kai wa bakin salati. (NAN).