✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole mu dage wajen kare darajar bangaren shari’a — Alkalin Alkalai

Ya bayyana cewa doka dai, doka ce, ko muradin wane ne wani al’amari ya shafa.

Alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Olukayode Ariwoola, ya ce dole ne alkalan kasar su tabbatar da kare daraja da kimar bangaren shari’a kamar yadda aka san su da shi kuma su tsaya tsayin daka wajen zama masu gaskiya da adalci a hukunce-hukuncensu.

Gidan talbijin na Channels TV ya ambato alkalin alkalan na wannan jawabi yayin bude zama na musamman na shekarar shari’a ta 2023/2024 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyi na Najeriya 58 a Abuja.

Mai shari’a Ariwoola ya kara da cewa yana tsammanin kowannen alkali zai yi aiki tukuru kuma ya kasance mai gaskiya da mutunta masu kararraki, da shaidu da kuma lauyoyi, sannan su gudanar da shari’o’insu da yin kas-kasa da kai cikin ikon da suke da shi.

Da yake alkawarta kare mulkin doka da ’yancin cin gashin kai na bangaren shari’a da kuma amana da kwarin gwiwar da al’umma ke da shi a kan bangaren, alkalin alkalan na Najeriya ya jaddada kudurin cewa bangaren shari’a ba zai damu kansa da ka-ce-na-cen mutane har su yi tasiri a hukunce-hukuncensu ba.

Ya bayyana cewa doka dai, doka ce, ko muradin wane ne wani al’amari ya shafa.

A baya-bayan nan, bangaren shari’ar Najeriya ya fuskanci zazzafar suka daga musamman ’yan adawar kasar, inda suke zargin wasu alkalai da zartar da hukunce-hukuncen da za su yi wa gwamnati da jam’iyya mai mulki dadi a shari’o’in zabukan kasar.

Sai dai jam’iyya mai mulki ta sha musanta haka, tana kalubalantar ’yan adawan da cewa ba sa yin irin wannan zargi, a wuraren da kotuna suka ba su nasara.