✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a saita al’amuran bangaren shari’a a Najeriya — Dattawan Arewa

An jaddada bukatar bangaren shari'a ya yi taka-tsan-tsan domin kare kansa daga zubewar mutunci da kima.

Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ta yi kiran a saita al’amura tana mai bayyana damuwa kan yanayin da bangaren shari’ar kasar nan ya shiga.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya fitar ranar Alhamis, ya jaddada bukatar bangaren shari’a ya yi taka-tsan-tsan domin kare kansa daga zubewar mutunci da kima la’akari da yardar da mutane ke yi wa bangaren.

Ya ce, “game da jawabin tsohon Babban Alkalin Kotun Koli, Dattijo Muhammad ya yi kan yadda rashawa ta dabaibaye fannin shari’a, kungiyar mu tana son ganin an inganta fannin shari’a domin wanzuwar dimokuraɗiyya.

“Kungiyar Dattawan Arewa ta ce ya zama dole a samu adalci a fannin shari’a kasancewarsa fannin mai zaman kansa da ke rike da gwamnati.

Ƙungiyar ta kuma ce rashin adalci da cin amanar aiki daga bangaren alkalai na bai wa ’yan siyasa ƙwarin gwiwar aiwatar da harkokinsu ta tsarin ko a mutu ko a yi rai.

Haka kuma, kungiyar ta ce yadda al’amuran shari’a ke gudana a baya bayan nan zai kara ingiza ’yan siyasar wajen cin karensu babu babbaka wajen ganin ko ta halin ka-ka sun kasance akan mulki.

“Kuma abin da muke gudu shi ne lalacewar fannin shari’a zai sa jama’a su debe tsammani a kan zabe, wanda hakan ke nuni da cewa wa’adin dimokuraɗiyya ya cika.

“A saboda haka muna kira ga bangaren shari’a ya duba muhimmancinsa a tsarin mulkin dimokuraɗiyya, ya tabbatar ya gudanar da ayyukansa na hukunce-hukunce cikin adalci, kuma ba sani-ba-sabo.”

Kungiyar ta kuma yi kira ga al’umma da su sanya ido kan ayyukan bangaren shari’a, domin hakan zai taimaka wajen al’amura sun daidaita.