✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole mu rage yawan ciyo bashi daga kasashen waje – Lawan

Kalaman na zuwa ne kasa da wata daya bayan Majalisa ta amince da bukatar ciyo sabon bashi.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya nemi a rage yawan ciyo bashi daga kasashen waje ta hanyar rage zirarewar kudade daga lalitar gwamnati.

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Kalaman nasa na zuwa ne kasa da wata daya bayan Majalisar da yake jagoranci ta amince da bukatar Shugaba Buhari ta ciyo bashin Dalar Amurka biliyan 8.3 da kuma Yuro miliyan 490.

Lawan ya ce dole gwamnatoci a dukkan matakai su lalubo hanyoyi masu bullewa ga matsalar kin zuba kudaden shigarsu da wasu hukumomin ke yi ga lalitar gwamnati.

A cewarsa, “Mun kuma tattauna a kan wasu batutuwa da suka shafi shugabanci, musamman ta bangaren kara yawan kudaden shigar gwamnatoci a dukkan matakai.

“Akwai hukumomin gwamnati da dama da ba sa shigar da kudaden da suka samu cikin lalitar gwamnati, wannan kuma wani abu ne da ya zama wajibi mu kawo karshensa da gaggawa saboda muna so mu rage ciyo bashi daga waje.

“Idan akwai hanyoyin da za mu sami karin kudaden shiga domin rage cin bashi to ya zama dole mu yi haka.

“Wannan yana daya daga cikin abubuwan da mu da Shugaban Kasa muka amince, dole mu lalubo hanyoyin bunkasa kudaden shigarmu,” inji shi.

Lawan wanda ya kuma ce sun tattauna a kan kasafin kudin 2022, ya ce akwai kwakkwaran tanadi ga harkar tsaro da manyan ayyuka kamar na Gadar Neja ta Biyu da aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano da ma wasu.

Ya ce babban a yanzu burinsu bai wuce ganin an kammala wadannan ayyukan nan da 2022 ba domin Buhari ya sami damar bude su don amfanin ’yan Najeriya.