✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dole ’yan magani su koma kasuwar Dan Gwauro a watan Fabrairu – Gwamnatin Kano

Gwamnatin ta ce babu gudu babu ja da baya

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba gudu ba ja da baya kan batun mayar da masu sayar da magani kasuwar duniya ta Dan Gwauro ranar 10 ga watan Fabrairu mai zuwa.

Kwamishinan Kasuwanci na Jihar, Barista Ibrahim Muktar ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da filin Inda Ranka na gidan rediyon Freedom da ke Kano, inda ya ce gwamnatin ta riga ta kammala duk wani shirin da ya kamata na tarewarsu.

A cewar Kwamishinan, “Ka san mutane ba sa son canji daga wajen da suka saba, ko mai kyau ne ko mara kyau ne, sai daga baya zaka ga an zo ana rububin komawa can.

“Duk da muna sane da masu kokarin yin zagon kasa ga irin wannan shirin. Su kuma ba za mu kyale su ba idan muka zakulo su.

Sai dai wasu daga cikin ’yan kasuwar sun koka kan rashin wadatattun rumfunan da za su dauke su a sabuwar kasuwar.

“Muna neman wata alfarma a matsayinmu na masu kananan karfi a kasuwar ’yan magani.

Wannan guri ya yi karanci, kuma yanzu haka a cikin kaso 100 na ’yan kasuwar, ba na jin kaso 17 sun samu wurin zama.

“Don haka muna rokon gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka mana a kara wa’adin da za mu samu damar shiga wurin cikin nutsuwa”, in ji wani dan kasuwa.

“Wannan shirin na gwamnati ya biyo bayan korafin da al’umma ke yi tsawon lokaci cewa ’yan kasuwar na fake wa da sana’ ar suna sayar da jabun magunguna da miyagun kwayoyi ga masu shaye-shaye,” in ji Kwamshinan.

Kasuwar ta Da Gwauro dai na dab da shiga Kano ne a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kuma tuni aka kammala kaso mai yawa na shagunan cikinta.