✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubun matafiyin da ya hadiye hodar Iblis ta N360m ta cika a Legas

Rahotanni sun ce nauyin hodar ya kai kimanin Kilogiram 1.55, kuma darajarta ta kai kusan Naira miliyan 360.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammad dake Legas sun cafke wani gawurtaccen mai safarar miyagun kwayoyi, Chigbogu Ernest Obiora.

An dai kama Chigbogu ne da kulli 97 na Hodar Iblis din da ya hadiye, sannan aka tilasta masa yin kashinta.

Rahotanni sun ce nauyin hodar ya kai kimanin Kilogiram 1.55, kuma darajarta ta kai kusan Naira miliyan 360.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya ce dubun mutumin ta cika ne ranar Lahadi, jim kadan da saukar wani jirgin kamfanin Ethiopian Airlines wanda ya sauka a Legas daga kasar Uganda.

Femi ya kuma ambato kwamandan hukumar reshen filin jirgin, Ahmadu Garba yana cewa
“Mun kai wanda muke zargi zuwa wajen injin dake ganin mutum har hanji, inda bayan sakamako ya nuna ya hadiyi hodar, muka tura shi zuwa wurin da NDLEA ta tanada don kasayar da ita.”

Da yake tsokaci a kan kamen, shugaban hukumar NDLEA na kasa, Birgediya Janar Nuna Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an hukumar dake filin jirgin saboda wannan gagarumar nasarar.

Ya kuma shawarci sauran jami’an dake sauran shiyyoyi da su kara jajircewa wajen ganin Najeriya ta yi bankwana da ta’ammali da miyagun kwayoyi baki daya.