✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Auwalu Daudawa: An harbe mutumin da ya kitsa sace Daliban Kankara

Auwalu Daudawa ya yi gamo da karshensa a hannun abokan adawa.

Auwalu Daudawa, mutumin da a baya bayan nan ya shahara bayan ta bayyana cewa shi ne ya kitsa kuma jagoranci sace Daliban Sakandiren Kimiyya ta garin Kankara a Jihar Katsina, ya yi gamo da karshensa a hannun abokan adawa.

Wata majiya mai karfi ta shaida wa Aminiya cewa, an kashe Auwalu Daudawa da yammacin ranar Juma’a yayin musayar wuta da wasu gungun abokan adawa a dajin Dumburum da ke tsakanin Karamar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara da kuma Karamar Hukumar Batsari da ke Jihar Katsina.

Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa, an kashe Daudawa ne a yayin da ya jagoranci wasu mayakansa a wani hari na ramuwar gayya kan mayakan wani abokin adawarwsa da ake yi wa lakabi da Ballolo.

Rahotanni sun bayyana cewa, a yayin da Daudawa ke zamansa a cikin garin Gusau sakamakon tuban da ya yi, wasu mayakan Ballolo sun kai wa nasa mayakan hari a kokarinsu na satar shanu, inda suka kashe biyu daga cikinsu.

Dalilin haka ya sanya Daudawa ya fusata da cewa ba zai bari wannan ta wuce ba, kuma ya sha alwashin ramawa kura aniyarta.

Majiyar rahoton ta tabbatar da cewa, karar kwana ta cimma Daudawa ne a hannun mayakan Ballolo wadanda suka yi masa ruwan harsasai yayin da aka fita filin daga a kokarinsa na ramuwar gayya.

Aminiya ta ruwaito cewa, kwanaki hudu da suka gabata ne Daudawa ya sake daukar makamai, inda ya koma kan ta’adarsa kasa da wata uku bayan ya bayyana tubarsa.

Rahoton ya bayyana cewa, a ranar Litinin ce Daudawa ya kwashe iyalansa da wasu yaransa suka koma Dajin Jaja da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.