✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Dubun mutumin da ake zargi da hada bama-bamai ta cika a Taraba

Ana zargin mutumin da yin amfani da gidansa a matsayin masana'anta

’Yan sanda a Jihar Taraba sun cafke wani mutumi da ake zargin ya kware sosai wajen harhada bama-bamai a cikin gidansa.

Dubun mutumin ta cika ne a garin Tella da ke Karamar Hukumar Gassol ta Jihar.

Aminiya ta gano cewa ’yan sandan sun kuma gano tarin wasu sinadaran hada bama-baman a gidan mutumin, inda ake zargin yana amfani da shi a matsayin masana’antar kera su.

Kazalika, an kama bindigogi da albarusai da dama a hannun shi.

Mutumin wanda dan asalin Jihar Zamfara ne dai yanzu haka yana hedkwatar ’yan sandan Jihar da ke Jalingo.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da kamun, ko da yake bai yi wani karin haske ba a kai.

Jihar Taraba dai a ’yan makonnin nan ta sha fama da fashe-fashen abubuwa har sau uku a wurare daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum takwas.

Kazalika, ’yan bindiga sun mamaye yankuna da dama a Karamar Hukumar Gassol sannan suka hana manoma zuwa gonakinsu.