✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai ya sallami hadimansa 19

Ya ce rukunin farko na masu rike da mukaman siyasa da zai sallama ke nan.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sallami mutum 19 daga cikin hadimansa a abin da gwamnatinsa ta kira rukunin farko na masu rike da mukaman siyasan da za a kora a aikin sallamar ma’aikatan da gwamnatin ke yi.

El-Rufai ya gamu da suka saboda korar dubban ma’aikata daga bakin aikin da ya yi a shirinsa na rage kudaden da gwamnatin jihar ke kashewa wurin biyan albasihin ma’aikata.

Ya sha nanata cewa gwamnaitn ba za ta ci gaba da kashe fiye da kashi 80% na kason da take samu daga Gwamnatin Tarayya ba wajen biyan albashin ma’aikata; yana mai cewa masu rike da mukaman siyasar ma matakin zai fada kansu.

A ranar Talatar gwamnatin ta sanar da sallamar masu rike da mukaman siyasa 19 ciki har da Mataimakin Shugaban Ma’aikatan gwamnan da masu ba da shawara na musamman guda biyu da sauransu.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, El-Rufai ya gode wa ’yan siyasar kan hidimar da suka yi wa jihar sannan ya yi musu fatan Allah Ya sa gaba ta fi baya kyau.

 Jerin sunayen wadanda aka sallamar:

 1. Bala Yunusa Mohammed
 2. Halima Musa Nagogo
 3. Umar Abubakar
 4. Ben Kure
 5. Mustapha Lynda Nyusha
 6. Jamilu Gwarzala Dan Mutum
 7. Umar Haruna
 8. Zainab Shehu
 9. Stephen Hezron
 10. Mohammed Bello Shuaibu
 11. Aliyu Haruna
 12. Halima Idris
 13. Injiniya Aliyu Alhaji Salihu
 14. Ashiru Zuntu
 15. Saida Sa’ad
 16. Elias Yahaya
 17. Tasiu Suleiman Yakaii
 18. Samuel Hadwayah
 19. Ahmed Mohammed Gero.