✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emefiele ya sake kai wa Buhari ziyara a sirrance

Wannan dai ita ce ziyara ta biyu kuma cikin sirri da Emefiele ya kai wa Shugaba Buhari cikin mako daya.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin  Emefiele, ya shiga bayan labule tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Aso Villa da ke Abuja.

Bayanai sun ce wannan dai ita ce ziyara ta biyu kuma cikin sirri da Gwamnan Babban Bankin Kasar ya kai wa Shugaba Buhari tun bayan dawowarsa Najeriya a ranar 12 ga watan Janairu.

Wannan ziyara na zuwa ne bayan Emefiele ya halarci taron Bankin Bunkasa Tattalin Arziki na Daular Larabawa wanda Darekta Janar na bankin, Dokta Sidi Ould Tah ya jagoranta a ranar Alhamis.

Tun a bara dai labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soma yamutsa hazo bayan da aka rika rade-radin cewa jami’an tsaron na sirri na nemansa ruwa a jallo.

A makonnin bayan nan ne dai Emefiele ya bar kasar biyo bayan binciken wasu zarge-zarge da ake yi masa, da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma samar da kudade ga ayyukan ta’addanci.

Sai dai tuni CBN ya kore wannan zargi yana mai cewa Emefiele ya ketare kasar nan saboda dalilai na hutun karshen shekara da doka ta ba shi dama.

Gabanin wannan dai, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta nemi wata Babbar Kotun ta sahale mata cafke Emefiele, amma Alkalin kotun, M.A. Hassan ya yanke hukuncin sanya shamaki tsakanin DSS din da Emefiele.

Kotu ta yi sammacin Emefiele

A Talatar wannan mako ce wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi sammaci Gwamnan Babban Bankin, inda ta nemi ya bayyana gabanta a jiya Laraba dangane da shari’ar sama da Dalar Amurka miliyan 53 na kudaden ‘Paris Club’.

Wannan dai na zuwa ne tun bayan wata kara da aka shigar gaban kotun a ranar 20 ga watan Oktoban 2022, lamarin da ya sanya Mai Shari’a Inyang Ekwo ya bai wa Emefiele umarnin ya bayyana a gabansa a ranar 18 ga Janairu don sauraron shari’ar.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar da lauya Joe Agi, ya shigar ne kan kamfanin Linas International Ltd da Ministar Kudi da CBN ta hannun lauyoyinsa, Isaac Ekpa da Chinonso Obasi.

A cikin karar, yana neman kotu ta bai wa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda umarnin cafke Emefiele da lauyoyinsa tare da gabatar da su a gaban kuliya.

Sai dai Emefiele ya daukaka kara a kan hukuncin Babbar Kotun, inda ya ce Mai Shari’a Ekwo ya yi kuskure a hukuncin tilasta halartar zaman kotun kan badakalar bashin dala miliyan 53.

A bisa wannan dalili ne dai zaman kotun na ranar Laraba bai wakana ba kamar yadda aka tsara, inda kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 20 ga watan Maris na 2023.