✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: An kama mutanen da suka kona wata Sakatariya a Legas

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta yi holin wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassan jihar. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Hakeem…

Rundunar Yan Sandan Jihar Legas ta yi holin wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassan jihar.

Kwamishinan Yan Sandan Jihar, Hakeem Odumosu, ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wadanta ake zargin a hedikwatar rundunar .

Ya ce jamian rundunar sun cafke wasu mutum uku da ake zargi yan kungiyar ne da aikata taaddanci a yankunan jihar.

Yan sandan sun bayyana cewa gogan cikinsu yana daga cikin yan taaddar yankin Lamgbasa, su kuma ragowar mutum biyun “sun rasa ransu sakamakom kisan da ya yi musu saboda ba sa aiki yadda ya kamata”.

A wani labari makamancin wannan kuma, rundunar ta kama wasu masu laifin da bindigar hannu kirar gida.

An kuma kama wasu mutum 10 da ake zargi da bankawa Sakatariyar Karamar Hukumar Ajeromi Ifelodun wuta yayin zanga-zangar #EndSARS.

Kwamishinan ’yan sandan jihar ya ce za a gurfanar da dukkannin wadanda ake zargi da aikata laifin a gaban kotu.