✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Euro 2020: UEFA na bincike kan magoya bayan Ingila

Ingila ta shafe shekara 55 ba tare da samun nasarar zuwa wasan karshe na kowace gasa ba.

Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta fara gudanar da bincike a kan yadda magoya bayan Ingila suka karya matakan tsaro a wasan karshe na gasar Euro 2020 da aka buga a filin wasa na Wembley, ranar Lahadi.

Wasu daga cikin magoya bayan na Ingila, sun yi kokarin kutsawa cikin filin wasan duk da rashin tikitin shiga .

  1. Za a fara daure barayin akwatin zabe shekara 20
  2. An kashe mutum 222, an yi wa 20 fyade a wata 3 a Kaduna – Rahoto

Amma jami’an tsaro sun yi namijin kokari wajen yin dauki-ba-dadi da su kafin daga bisani su cimma su.

A wasan karshe na gasar Ingila ta yi rashin nasara a hannun Italiya a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-raga.

Ingila ta shafe shekara 55 kafin samun nasarar zuwa wasan karshe na kowace gasa a kwallon kafa a duniya.