✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Farashin Dala zai fadi warwas a Najeriya

Bankuna sun bayar da tabbacin cewa farashin Dala zai koma N423.

Bankuna sun bayar da tabbacin cewa farashin canjin Dala a Najeriya zai koma N423.

Shugabannin bankunan sun bayar da tabbacin ne ranar Alhamis, washegarin da Dala ta yi tashin gwauron zabo zuwa fiye da N523 a kasuwar canji ta bayan fage.

Tashin farashin Dala a Najeriya ya zo ne bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shirinsa na mayar harkar canji zuwa bankunan kasuwanci tare da dakatar da ba wa kamfanonin canjin kudaden kashen waje Dala, kamar yadda ya saba.

Amma Shugaban Kwamitin Bankuna na Najeriya kuma Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe ya bayar da tabbacin cewa farashin zai sauka zuwa N423.

Ya yi bayanin ne bayan ganawarsu da CBN kwana biyu bayan Babban Bankin ya sanar da matakin da ya hada da dakatar yin rajistar sabbin kamfanonin canjin kudade.

SAURAI: Tasirin hana wa ’yan canji Dala:

Da yake jawabi kan tashin Dala zuwa N523 Shugaban Guarantee Holdco (GTCo) ya ce: “Abin da muka ganin a kasuwar canji jiya ba mai dorewa ba ne.

“Farasin zai sauka nan ba da dadewa ba za ku fara sayen ta a kan N423 zuwa N425.”

A cewarsa, nan gaba kowa zai iya shiga cikin banki ya bukaci a ba shi canjin Dala.

Wigwe ya ce CBN ya umarci bankuna su kafa sashen kula da canjin kudaden kasashen waje.

“Babu abin da bankuna za su caji mutum saboda sun ba shi canji,” inji shi.