✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya yi wa matasa masu neman aikin soja alawus a duk wata

Gwamnan ya yi musu alkawari alawus a duk wata har su fara aikin soja.

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya ba da tallafin Naira miliyan 12.8 ga matasa ’yan asalin Jihar su 641 da ake tantancewa domin zama kuratan sojoji.

Zulum ya ziyarce matasan ne a Barikin Sojoji na Maimalari da ke Maiduguri inda ya sa a ba wa kowannensu Naira 20,000.

Gwamnan ya kuma ba da umarnin biyan kowanne daga cikin matasan N15,000 a duk wata a matsayin alawus a tsawon lokacin da za su yi a makarantar horas da kuratan sojoji (DEPOT) da ke Zariya.

Matasan su ne wadanda suka tsallake matakai daban-daban na gwaje-gwajen lafiyar da dangoginsu, kuma nan ba da dadewa ba za a kai su Dajin Falgore domin tantancewar karshe, kafin a kai su DEPOT.

Zulum, wanda Kwamandan Rundunar Operation Hadin Kai, Manjo-Janar Christopher Musa ya karbi bakuncinsa, ya yi kira ga matasan “Kar ku sake ku aikata ba daidai ba a ko’ina. Allah Ya yarda za mu ba ku duk goyon bayan da ake bukata”.