✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farashin danyen mai ya kara tashi a kasuwannin duniya

Putin ya ce da kudin Rasha na Ruble kadai kasashen Yammacin Duniya za su sayi gas.

Farashin danyen man fetur ya kara tashi a kasuwannin duniya a sakamakon mamayar da Rasha ke yi a kasar Ukraine.

Wannan dai na zuwa ne a sakamakon faduwar hannayen jari saboda fargabar daina sayen makamashin Rasha da kuma hauhawan farashinsu.

Rahotanni sun ce farashin man ya tashi da sama da kashi 4 a kasuwannin duniya, inda a ranar Laraba aka sayar da kowacce ganga akan sama da dala 120.

Mataimakin Firaministan Rasha, Alexander Novak ya yi gargadin cewa haramta sayen makamashin Rasha kamar yadda kasashen Yammacin duniya ke bukatar ganin anyi, na iya ruguza kasuwar makamashin baki daya.

Novak da ke jawabi ga Majalisar Wakilan Rasha ya ce babu wanda zai iya hasashen yadda farashin makamashin zai ci gaba da tashi a fadin duniya.

A bangare daya, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa daga yanzu kudin kasar na Ruble kawai kasashen yammacin duniya za su yi amfani da shi wajen sayen mai da iskar gas a Rasha.

Putin ya ba Babban Bankin Rasha mako daya ya samar da hanyar da za a sauya tsarin biyan kudin na Rasha maimakon wasu kudaden.