✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Yusuf ya zama Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya

Wa'adinsa na farko a ya fara daga ranar 3 ga Satumba, 2021

Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya zama sabon Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya (NAEC), bayan amincewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sanarwar hakan da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya fitar ta ce wa’adin farko mai tsawon shekara uku ke nan da Farfesa Yusuf zai yi a matsayin shugaban hukumar.

“Kafin yanzu, Farfesa Yusuf Aminu Ahmed shi ne Daraktan Lura da Ofishin Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya.

“Farfesa ne a fannin Kimiyyar Sanadaran Nukiliya ya kuma shafe tsawon shekaru a wasu bangarori na wannan fanni na kimiyya,” inji sanarwar da Daraktan Yada Labaran Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey, ya fitar.

Sanarwar da aka fitar ranar Juma’a da dare ta ce nadin na Farfesa Yusuf ya fara aiki ne daga ranar 3 ga watan Satumba, 2021.

A shekarar 1976 aka kafa Hukumar Makamashin Nukiliya ta Najeriya domin ginawa da kuma kula da kayayyakin nukiliya a Najeriya.

Makasudin yin hakan shi ne kokarin samar da wutar lantarki da kuma gudanar da bincike kan hanyoyin amfani da makamashin ta hanyoyin da ba na yaki ba.

Akwai kuma batun horaswa da ilmantar da masu nazari a fannin makamashin nukiliya da dangoginsu.