✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasinja ya rasu a hatsarin mota a Abuja

Tayar motar ta fashe sannan ta fada rami.

Wani fasinja ya rasu yayin da wani ya samu rauni bayan da wata motar bas ta yi hatsari a Abaji da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Wani ganau ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:12 na safiyar Lahadi a lokacin da wata motar bas kirar J5 Peugeot dauke da tumatir tayarta ta fashe.

Ya ce hakan ya sanya motar kwacewa daga hannun direban ta fada a rami.

Ya ce jami’an Hukumar kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) sun isa wurin inda suka dauke gawar da wadanda suka jikkata zuwa asibiti a yankin.

Wani jami’in hukumar FRSC, wanda ya ce ba a shi izinin tattaunawa da manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya alakanta hatsrin da rashin kyawun taya da gudun wuce kima.

Ya ce an ajiye gawar fasinjan a babban asibitin Abaji, yayin da wanda ya jikkata kuma ake kula da lafiyarsa a asibitin.