✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasinjoji 14 sun kone kurmus a hatsarin motar hanyar Legas

Rahotanni dai sun ce wata motar haya ce ta daki wata lalatacciyar mota kirar Toyota RAV4 wacce aka ajiye a tsakiyar hanya

Kimanin fasinjoji 14 ne suka kone kurmus, ciki har da kananan yara uku sakamakon wani hatsarin mota a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Wakilinmu ya gano cewa wata mota kirar Toyota RAV4 mai lamba LND13GS da Toyota Camry mai lamba GGE369GJ da kuma wata Mazda wacce ba a kai ga tantance lambarta ba ne suka yi taho-mu-gama da misalin karfe 10:20 na daren ranar Alhamis.

Rahotanni dai sun ce wata motar haya ce ta daki wata lalatacciyar mota kirar Toyota RAV4 wacce aka ajiye a tsakiyar hanya a daidai lokacin da take kokarin gudu domin wuce sauran motoci a kan hanyar.

Daga nan ne ta kwace ta yi ta tintsirawa kafin daga bisani ta kama da wuta.

Kakakin Hukumar Kula da Kula da Bin Dokokin Hanya (TRACE), Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da faruwar hatsarin da safiyar Juma’a.

A cewarsa, fasinjoji 14 ne ciki har da kananan yara uku suka rasa rayuwarsu a sanadiyyar hatsarin.

“Gaba daya akwai jimlar fasinjoji 14 lokacin da hatsarin ya faru, uku suka ji mummunan rauni, 14 kuma suka kone kurmus, ko gane su ba a iya yi,” inji shi.

Ya ce daga nan ne jami’an hukumar ta TRACE da sauran jami’an tsaro suka garzaya da su Cibiyar Kiyaye Hadurra da Bayar da Agajin Gaggawa zuwa Babban Asibitin Gbagada a jihar Legas.

Daga nan sai hukumar ta gargadi direbobi a kan gudun wuce sa’a, kokarin wuce sauran motoci ba bisa ka’ida ba wanda kan jefa su cikin hatsari.