✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya zaftare albashin masu rike da mukaman siyasa a Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya zaftare kashi hamsin daga cikin dari na albashin masu rike da mukaman siyasa a Jihar Kano. Kwamishinan Yada Labarai na…

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya zaftare kashi hamsin daga cikin dari na albashin masu rike da mukaman siyasa a Jihar Kano.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin Talata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, daga cikin wadanda zaftarewar albashin za ta shafa ciki har da Mataimakin Gwamna, Kwamishinoni, Mashawarta da sauran Hadimai na Musamman ga Gwamnan.

Sauran sun hada da Shugabannin Kananan Hukumomi da Mataimakansu, Kansiloli da Sakatarorin Kananan Hukumomi .

Aminiya ta fahimci cewa, matakin hakan na zuwa ne bayan sa’a 24 da Gwamnatin Jihar Kano ta yi ikirarin cewa ba za ta iya biyan ma’aikata cikakken albashinsu ba na watan Maris saboda abin da ta danganta da raguwar kasafin kudi da Gwamnatin Tarayya ke bai wa jihohi.

Sai dai tuni Kungiyar Kwadago reshen jihar ta yi tutsu a kan lamarin, inda ta misalta matakin da Gwamnatin ta dauka a matsayin rashin adalci tare da ba ta wa’adin kwanaki bakwai ta mayar wa da ma’aikatan albashinsu da ta zaftare.

Kungiyar kwadagon ta ce muddin gwamnatin ta hau kujerar naki a kan mayar wa da ma’aikatan albashinsu, to kuwa za su gurgunta lamura a jihar ta hanyar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki uku.

A watan Maris da ta gabata ne Gwamnatin Jihar Kano ta karbi Naira biliyan 12.4 daga kasafin da Gwamnatin Tarayya ke bai wa jihohi, wanda daga ciki Naira biliyan 6.1 shi ne na ta, yayin da kuma Kananan Hukumomin Jihar 44 za su rarraba Naira biliyan 6.3 a tsakaninsu.

Sai dai Gwamnatin ta ce ba ta sukunin biyan cikakken albashin ma’aikata madamar ba ta samu karin wasu biliyoyin naira ba wanda a yanzu haka ba ta da halinsu.