✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai kafa hukumar kula da magungunan gargajiya a Kano

Gwamnatin jihar Kano na shirye-shiryen samar da hukumar da za ta rika kula da masu magungunan gargajiya a jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata…

Gwamnatin jihar Kano na shirye-shiryen samar da hukumar da za ta rika kula da masu magungunan gargajiya a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Mataimakin Gwamnan Jihar, Hassan Musa Fagge ya fitar ranar Laraba.

Ya ce Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin karbar tawagar Hukumar Lafiya ta kasa, a fadar gwamnatin jihar.

Daraktar Sashen kula da Magungunan Gargajiya da Makamantansu (TCAM) ta hukumar, Hajiya Zainab Ujudud-Sharif ta ce makasudin ziyarar shi ne yaukaka alaka tsakaninsu da gwamnatin, domin kafa reshenta a jihar.

A nasa bangaren, Gwamnan, wanda Mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta, ya ce Gwamnatin za ta assasa sashen na TCAM, domin daidaita magunan sun zamo na bai daya.

Haka kuma, ya umarci wakilan hukumar na tarayya da su rubuto takardar da zai gabatar wa Majalisar zartarwar jihar, don assasa sabuwar hukumar.

“Jihar Kano na cike da albarkatun noma, musamman abubuwan da aka fi magani da su irin su albasa da citta da kanimfari da tafarnuwa da sauransu.

“Haka kuma, tsirran da aka fitar daga Kano, sun fi kyau da inganci, idan aka kwatanta su da na kasashen waje.

A karshe Zainab Ujudud-Sharif ta yaba wa Gwamnatin jihar, bisa wannan yunkuri da ta yi domin kare lafiyar al’ummar jihar, tare da fatan za ta cika wannan alkawarin.