✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara a sansanin ’yan gudun hijirar Borno ta hallaka jariri, ta kona gidaje 620

Wani shaidar gani da ido ya ce gobarar ta ranar Laraba ta samo asali ne daga iskar hunturu.

Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira dake kan hanyar Mafa a Maidugurin jihar Borno ta yi sanadiyyar mutuwar wani jariri tare da kone tantuna 620.

Wani shaidar gani da ido ya ce gobarar, wacce ta samo asali daga wata iskar hunturu da aka yi ta fara ne da misalin karfe 7:30 na safiyar Laraba.

A cewar majiyar, “Wajen misalin karfe daya na rana wata wutar ta sake tashi inda ta kone wasu tantuna a sansanin. Wani jariri ya kone kurmus, sai kuma wasu mutum biyu da suka sami raunuka.”

Gaba daya dai rahotanni sun ce yawan tantunan da suka kone ya kai 620 kuma jami’an hukumomin kashe gobara na tarayya da na jihar ne suka hada gwiwa wajen kashe ta.

Mai rikon mukamin Jami’in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) shiyyar Arewa Maso Gabas dake birnin Maiduguri, Ishaya Chinoko ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma ce sun gudanar da bincike da hadin gwaiwar Hukumar Bayar Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (BOSEMA) da sauran kungiyoyin jinkai domin kiyasta irin barnar da gobarar ta yi don su tallafawa wadanda suke cikin tsananin bukata.

Ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a rarraba musu kayan tallafi domin su rage radadin mawuyacin halin da suka shiga.

Sansanin dai na da jimlar ’yan gudun hijira 14,250 wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu daga Kananan Hukumomin Dikwa, Mafa da Bama.