✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar daji ta kashe soja 25 da wasu 22 a Algeria

An kama muutm hudu kan zargin ta da wutar a Gabashin Algiers, babban birnin kasar.

Akalla mutum 42, ciki har da sojoji 25 ne aka tabbatar sun rasu a gobarar dajin da ta tashi a kasar Algeria.

Firai Minitan kasar, Ayman Benabderrahmane, ya ce sojojin sun kwanta dama ne a yayin da suke aikin ceton mutane a gagarumar gobarar da ke ci a yankin Gabashin Algiers, babban birnin kasar.

Shugaban Kasar, Abdelmadjid Tebboune ya wallafa sakon ta’aziyyar sojojin ya ce, “Na kadu matuka da samun labarin mutuwar shahadar da sojojinmu 25 suka yi bayan sun yi nasara ceto sama da mutum 100 daga wutar daji daga tsaunukan Bejaia da Tizi Ouzou”

Ma’aikatar Tsaron Algeria ta ce “sojojin su 25 sun yi nasarar ceto mata da kananan yara da mazaje 110 daga gobara” a yankunan Bejaiea da Tizi Ouzou inda wutar ta fi kamari.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP a Tizi Ouzou ya ce ya ga jami’an kiwon lafiya na daukar gawarwaki, wasunsu a kokkone.

Algeria ta shiga jerin kasashen da a baya-bayan nan suka yi fama manyan gobarar daji da suka haka da Amurka da Rasha da Turkiyya da Greece da kuma Cyprus.

– Mutum 4 sun shiga hannu

Gwamnatin kasar na zargin mutane ne suka haddasa gobarar, har sun cafke wasu daga cikin wadanda zargi da tayar da wutar.

Gidan rediyon gwamnatin kasar ta ce an kama mutum uku kan tayar da gobarar a Arewacin lardin Medea da kuma muutm daya a Annaba.

Wurare akalla 70 aka samu tashin rin wannan gobara a jihohi 14 da ke Arewacin kasar, kuma 10 cikinsu a Tizi Ouzou, gari mafi yawan al’umma a yankin Kabylie.

A yayin ziyarsa ga garin da ke Arewacin kasar, Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar, Kamel Beldjoud, ya shaida wa manema labarai cewa “Babu yadda za a yi haka kawai gobarar daji ta tashi a wurare sama da 50 a lokaci guda. Dole akwai hannun masu aikata miyagun laifuka”.

Hukumomin kasar sun kara da cewa wutar ta shafi birane 12 da ke Arewacin kasar mai fama da karancin ruwa, inda kuma a halin yanzu zafin rana ya kai digiri 46.