✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda gobarar daji ta kwana 6 tana barna a kasashen Turai

Wutar ta kwana shida tana ci a dazukan Kudancin birin Bordeaux na kasar Faransa

Gobarar daji ta shafe kwana shida tana ci babu kakkautawa a dazukan Kudancin birin Bordeaux na kasar Faransa.

Kawo yanzu, jami’an ceto sun kwashe dubban mutane daga gidajensu a kasashen Faransa da Andalus da Portugal, inda gobarar daji ke ci gaba da barna.

Dubban jami’an kashe gobara sun shafe tsawon ranar Lahadi suna kokarin shawo kan wutar a kasashen.

Sojoji da jami’an kwana-kwana a Andalus na kokarin kashe wutar da ta tashi a wurare sama da 30 a dazukan da ke fadin kasar.

A Faransa kuwa, wutar ta kwana shida tana ci a dazukan Kudancin birin Bordeaux da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Gobarar dajin ta tilasta wa akalla mutum 14,ooo yin kaura daga muhallansu, ciki har da wadanda suka je yin hutu a yankin.

Ma’aikatan kashe gobara akalla 1,200 ne ake girke domin shawon wutar da ke ci gaba da barna a yankin Gironde a kasar.

Gobarar ta kuma cinye kasa mai fadin sama da hekta 37,000 na dazukan kasar Portugal.

Wani matukin jirgin kashe gobara ya rasu a yayin aikin kashe gobarar bayan jirginsa ya yi hatsari a Arewa maso Gabashin kasar.

Akalla mutum 160 ne wutar daji ta jikkata a wannan karon a Portugal baya ga daruruwa da suka yi kaura daga gidajensu.

Nahiyar Turai dai na fama da matsanancin zafi da hukumomi ke hasashen zai haddasa yawan mace-mace.

Hukumomin Turai na hasashen zuwa farkon makon gobe tsananin zafin zai haura na kowane lokaci.

Cibiyar Meteo France ta yi hasashen za a fara samun matsanancin zafin ne daga ranar Litinin.