✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobarar tankar mai ta hallaka mutum biyar a Neja

Wata gobara ta rutsa da mutum 5 tare da raunata wasu da dama a Karamar Hukumar Lapai, Jihar Neja. Gobarar da ta tashi da safiyar…

Wata gobara ta rutsa da mutum 5 tare da raunata wasu da dama a Karamar Hukumar Lapai, Jihar Neja.

Gobarar da ta tashi da safiyar Talata to cinye akalla ababen hawa bakwai ciki har da tankokin mai guda biyu makare da fetir da wasu tankokin iskar gas biyu.

Ganau sun ce, “Mutum shida sun kone kurmus, hudu daga cikinsu an dauke su a motar daukar marasa lafiya ta Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC), wasu biyar da suka samu kuna kuma an kai su Agaie domin samun kulawa”.

Sun ci gaba da bayyana cewa ragowar abubuwan da gobarar ta rutsa da su sun hada da sundukai da wata motar bus.

Shugaban Hukumar Agaji ta Jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Inga wanda ya ziyarci wurin ya ce lamarin ya auku ne bayan tankar fetur din ta fadi man da ke cikinta ya tsiyaya a kan hanya.