✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 20 a Delta

Mazauna sun rika dibar man fetur din da ya rika kwarara bayan kiferwar tankar man.

Akalla mutum 20 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hadarin gobarar tankokin man fetur da ya auku safiyar wannan Lahadin a Jihar Delta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kwanar Kokon daura da Gadar Ologbo da ke kan babbar hanyar Warri zuwa Benin a Karamar Hukumar Warri ta Arewa.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra reshen Jihar Delta, Udeme Bassey Eshiet ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai a cewarsa, hadarin ya rutsa da mutum 15 ciki 8 sun riga mu gidan gaskiya yayin da bakwai suka samu raunuka.

Kwamandan ya ce wadanda karar kwana ta cimma sun kone kurmus sakamakon hadarin da ya auku tsakanin motoci 15 ciki har da tankokin mai takwas.

Ya alakanta aukuwar hadarin da fashewar wata tankar mai daya wanda ya ce tuni jami’ansu da takwarorinsu na hukumar ’yan sanda sun rufe hanyar.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa, akalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hadarin

Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce daga cikin wadanda ajalin ya katsewa hanzari har da wata mai juna biyu, kananan yara da kuma wasu dattawa.

Ya ce bayan faduwar tankar ce man da ta dauko dakonsa ya rika kwarara a kan hanya, lamarin da ya sanya wasu suka rika rige-rigen diban rabonsu duk da gardadin da direban motar da jami’an tsaro suka yi.

“Mun yi kokarin hana su, amma wasu matasa suka yi mana barazanar lakada mana duka da cewar ai unguwarsu ce.

“Sun debo mazubi iri-iri suna dibar man amma muna samun labarin tashin gobarar da misalin karfe 12:15 na dare muka tsere.

“A yanzu dai ga gawarwaki nan kwance, an tsinto gawarwakin wasu da suka tsere cikin daji suna ci da wuta don ko a yanzu na kirga gawarwakin fiye da 20,” a cewarsa.