Greenfield: ‘Yan sanda sun cafke mutum 2 da bindigogi 41 | Aminiya

Greenfield: ‘Yan sanda sun cafke mutum 2 da bindigogi 41

A general view of the gate of the Greenfield University in Kaduna, Nigeria, on April 21, 2021. – Gunmen have attacked a private university in Nigeria’s northern Kaduna state, killing one staff member and kidnapping some students, police and officials said on April 21, 2021.
It was not immediately clear how many students had been abducted from Greenfield University during the April 20, 2021 attack at night and one official said they were still conducting a headcount. (Photo by NASU BORI / AFP) (Photo by NASU BORI/AFP via Getty Images)
A general view of the gate of the Greenfield University in Kaduna, Nigeria, on April 21, 2021. – Gunmen have attacked a private university in Nigeria’s northern Kaduna state, killing one staff member and kidnapping some students, police and officials said on April 21, 2021. It was not immediately clear how many students had been abducted from Greenfield University during the April 20, 2021 attack at night and one official said they were still conducting a headcount. (Photo by NASU BORI / AFP) (Photo by NASU BORI/AFP via Getty Images)
    Bashir Isah

’Yan sanda sun tabbatar da cafke wasu mutum biyu da ake zargin suna da hannu a garkuwa da aka yi da daliban Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan jihar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ne ya ba da tabbacin hakan ga manema labarai ranar Laraba a Abuja, yayin gabatar da su da sauran wadanda ake zargi a aikata manyan laifuka.

Kakakin ’yan sandan ya ce sun kwace makamai da dama a hannun masu garkuwar, ciki har da bindiga kirar AK guda 41 da tarin alburusai da sauransu a hannun bata-garin da suka shi hannu.

Game da masu garkuwa da daliban Greenfield, ya ce wadanda ake zargin sun yi ikirarin sun kashe biyar daga cikin daliban, sannan suka saki sauran bayan karbar kudin fansa.

Haka nan, Adejobi ya ce, wadanda ake zargin sun tabbatar cewa sun yi aiki tare da wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane wajen sace ’yan sanda biyu da dan banga daya a 2021.

Ya kara da cewa, jami’ansu sun kama wadanda ake zargin ne a watan Maris bayan da suka bibiye su kan sace daliban Makarantar Bethel Baptist da ke Jihar Kaduna a 2021.

Ya ce sun kuma kama wasu bata-gari su biyar da ke garkuwa da kwace dukiyar mutane a tsakanin Jihar Adamawa da wasu sassan kasar Kamaru.

Ya kara da cewa, su ma sun yi ikirarin yin garkuwa da mutane da dama da yi wa wata amarya fyade sannan daga bisani suka karbi fansar Naira miliyan daya kafin suka sake ta.

Kakakin ’yan sandan ya ce sun kwace makamai da dama a hannun masu garkuwar, ciki har da bindiga kirar AK guda 41 da tarin alburusai da sauransu.