✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gudun sharholiya ne ya dawo da ni daga Amurka ranar ‘birthday’ dina – Buhari

Ya ce ranar ba ta da bambanci da sauran ranakun aiki a wajensa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ma’aikatan fadarsa sun hana shi cika burinsa na yin bikin ranar zagayowar haihuwarsa salim -alim.

Buhari ya ce dalilin ke nan ma da ya sa da gangan ya sanya ranar dawowarsa daga Amurka ta kasance a ranar bikin.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da ma wasu daga cikin ma’aikatan fadar shugaban da suka taru don taya shi murna ranar Litinin.

Shugaban ya nuna godiyarsa da dimbin katinan taya shi murna da sakonnin fatan alheri kan cikarsa shekara 80 a duniya da ya yi ranar Lahadi.

Sai dai Buhari ya ce a wajensa, ranar ba ta da wani bambanci da sauran ranakun aiki.

A sakon da Farfesa Gambari ya karanta a madadin ragowar ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar, ya ce, “Muna alfahari da kai ya mai girma Shugaban Kasa saboda damar da ka ba mu ta hidimta wa Najeriya cikin girmamawa.”