✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Radda ya biya wa fursunoni 222 tara albarkacin bikin sallah

Ana tsare da waɗannan fursunoni ne saboda rashin iya biyan tarar da kotuna daban-daban suka sanya musu.

Gwamnan Katsina, Malam Umar Dikko Radda, ya biya wa wasu fursunoni 222 tara masu cin sarka a gidajen yari daban-daban da ke faɗin jihar.

Wannan wani yunƙuri ne na nuna tausayi ganin irin yadda watan Ramadana ya gudana sannan ga bukukuwan Sallah na zuwa.

Wata sanarwa da Ofishin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Fadar Gwamnatin Katsina ya raba wa manema labarai a ranar Litinin, ta ce ana tsare da waɗannan fursunoni ne saboda rashin iya biyan tarar da kotuna daban-daban suka sanya musu.

Sanarwar ta kuma ambato Babbar Lauyar Gwamnati kuma Kwamishinar Shari’a ta jihar, Barista Fadila Muhammad Dikko Esq na cewa wannan wani yunƙuri ne na bai wa fursunonin damar yin bukukuwan sallah tare da iyalansu.

Haka kuma, Kwamishinar ta ce wannan hobbasa wani yunƙuri daga ɓangaren Gwamna Radda da nufin rage cunkoso a gidajen kason da ake tsare da fursunonin.

Barista Fadila ta yaba da wannan karamcin wajen bayar da agaji ga wadanda ake tsare da su a kan ƙananan laifuffuka walau na bashi ko harkokin kasuwanci da sauransu.

Ta ƙara da cewa, an gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da tsari waɗanda za su ribauta da alherin gwamnan na sauke wa masu ƙananan laifuka nauyin tarar da ke wuyansu.

“Ana sa ran aikin alherin da Gwamna ya yi zai rage cunkoso a waɗannan gidaje da kuma bai wa fursunonin da aka sako damar shiga cikin bukukuwan Sallah tare da ‘yan uwa da abokan arziki.”