✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Kano: Na ci zaben dan takara, amma aka bai wa wanda ya zo na 3 —Muhammad Abacha

Mohammed Abacha ya ce ya lashe zaben dan takarar Gwamnan Kano amma aka maye gurbinsa da sunan wanda ya zo na uku

Muhammad Abacha, ya bukaci kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta bayyana shi a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar PDP.

Muhammad Abacha ya je Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ne yana kalubalantar gabatar da sunan Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar jam’iyyar da kuma zargin  da mutumin da ya zo na biyu a zaben, Jafar Sani Bello, ya yi cewa shi ba dan PDP ba ne.

Ya bukaci kotu ta hana INEC “Daukar sunan Sadiq Wali a matsayin dan takarar gwamnan Kano a PDP bayan mika wa mai kara sahihin takardar shaidar sunayen wadandan suka ci zaben ’yan takarar jam’iyyar, wanda INEC ta sanya iko a lokacin da aka gudanar, wadda ta bayyana mai kara a matsayin dan takarar gwamnan jamiyyar a Jihar Kano.”

Ya shaida wa kotun cewa shi ne ya lashe zaben da jam’iyyar ta gudanar ranar 25 ga watan Mayu, wanda INEC ta sanya ido a kai, da kuri’a 736, Ja’afar Sani Bello kuma 710, amma aka maye gurbin sunansa (Muhammad Abacha) da sunan Sadiq Aminu Wali.

Don haka ya bukaci kotun ta hana PDP da Shugabanta Jam’iyyar na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi daga gabatar da Sadiq Wali a matsayin dan takarar PDP na gwamnan Kano a zbaen 2023.

Ya kara da cewa shi halastaccen dan PDP ne, kuma ta yi masa afuwa ya tsaya takara sannan ta tantance shi a matsayin dan jam’iyya.

Sammacin da ya shigar ta hannun lauyoyinsa, J.Y. Musa (SAN) da Reuben Atabo (SAN), ta bayyana INEC da Sadiq Aminu Wali da Jam’iyyar PDP da kuma Shguaban jam’iyyar a jihar, Shehu Wada Sagagi a matsayin wadanda ake zargi.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Satumba, 2022.