✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Legas ya dauki nauyin karatun ’yan aikin mai kosai

Daya daga cikin yaran ta ce mahaifiyarta malamar makaranta ce amma tsadar kudin makaranta ya fi karfinsu

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya dauki nauyin karatun wasu kananan yara mata biyu da ke aiki a karkashin wata mai sana’ar tuyan kosai.

Amarachi Chinedu mai shekara tara da kuma Suwebat Husseini mai shekara 12, kakarsu ta yanke saka ne a lokacin da suke tsaka da zuwa kai wa mai kosan markade.

Ayarin motocin gwamnan ya yi kicibus da yaran ne a lokacin da yake wucewa a yankin Anthony Village, a daidai lokacin makaranta, inda gwamnan ya hango yaran da robobi niki-niki a kansu.

Nan take ya tsaya, ya inda tambaye su abin da ya sa ba su je makaranta ba, su kuma suka bayyana masa cewa iyayensu ne ba su da halin tura su zuwa makaranta, maimakon haka sai suke zuwa yin aiki wurin mai kosan.

Amarachi mai shekara tara ta shaida wa gwamnan cewa mahaifiyarta malamar makaranta ce, amma ba su da karfin sanya ta a makaranta saboda kudin makaranta ya yi tsada sosai.

Ita kuma Suwebat shaida masa cewa ’yan uwanta maza hudu suna zuwa makaranta, amma mahaifanta suka zabi ita ta rika zama tana taya su yin aikace-aikace a gida.

Ta bayyana masa cewa mahaifiyarta ce mai kosan, kuma ba su jima ba da zuwa Legas daga Jihar Jigawa.

Sanwo-Olu ya bayyana damuwarsa bisa ganin kananan yaran a haka, wanda ya ce kan iya jefa su a cikin mawuyacin rayuwa a nan gaba.

Ya ce saboda haka, daga aljihunsa zai dauki nauyin kula da su da kuma ilmantar da su domin tabbatar da sun ci gaba da karatu.

Aminiya ta gano cewa tuni dai aka sanar da iyayen yaran game da alkawarin  da gwamnan ya yi musu.

Hakan dai ya faru ne a lokaicn da gwamnan yake kan hanyarsa ta zuwa taron kaddamar da shirin tallafin kyautata rayuwa na SWIP a jihar.

Da yake jawabi a wurin taron, Sanwo-Olu ya ce abin da yaran suka fada masa ya dame shi sosai.

“Saboda haka na dauki alkawarin ganin cewa hakan ba ta sake faruwa da su ba, kuma ba zan bar su a haka ba, tabbas Amarachi da Suwebat za su koma makaranta,” inji shi.

Sai dai ya shawarci iyaye da su guji daukar nauyin da ya fi karfinsu na cewa dole sai sun sanya ’ya’yansu a makarantu masu tsada.

A cewarsa, akwai makarantun gwamnati da dama a Jihar Legas da suka fi na kudi inganci wurin samar da ilimi mai nagarta.