✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta soke sabon karin kudin lantarki

Minista ya ce ba a ba wa hukumar NERC izinin karin farashin da aka yi ba.

Ministan Lantarki, Injiniya Sale Mamman, ya ba da umarnin dakatar da sabon karin kudin wutar lantarki da aka yi har zuwa karshen watan Janairu 2021.

Ministan ya ce ba a wa Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) izinin karin kaso 50% na kudin wutar ba.

Injiniya Sale ya ce “bayan cimma matsaya a tattaunawar da muka yi da kungiyoyin kwadago, mun umarci NERC da ta sanar da kamfanonin rarraba wutar lantarki cewa su janye karin da suka yi.

“Wannan ita ce hanya kadai da za a samu kyakkyawan sakamako,” cewar Ministan.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ba ta tallafin kaso 55% ga masu samun wuta kasa da awa 12 a rana, wato rukunin D da E.

Sannan ya ce karin da ka yi a watan Disamban 2020, ya shafi rukunin A, B da C ne kadai, masu samun wuta na akalla awa 12 ne a rana.

Ya bayyana cewa wanda suke kan rukunin D da E ba sa cikin wadanda karin da aka yi a watan Disamban 2020 ya shafa.

Ministan ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ’yan Najeriya.

“Gwamanti da Ma’aikatar Wutar Lantarki za su ci gaba da samar da tsarin da zai taimaka wa marasa karfi da ingantacciyar wutar lantarki,” inji shi.