✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin APC ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya — Kwankwaso

Ya ce dole ’yan Najeriya su fatattaki APC a 2023

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce gwamnatin APC ta jefa Najeriya cikin mawuyacin hali sakamakon rashin iya jagoranci.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da Bishop Isaac Idahosa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 a Abuja.

Dan takarar ya kuma ce wadannan jagororin sun yi wa kasar munanan raunuka, musamman ma yankin Arewa sakamakon rashin gaskiya da sanin makamar jagoranci a kasar da ke da mabiya addinai da al’adu daban-daban irin Najeriya.

Ya ce, “Rashin gaskiyarsu da fahimta ya sanya suka raunata yankin da ma kasarmu baki daya. Rashin tausayinsu ga talakawa ya sanya kasar fadawa mawuyacin hali da ma al’ummar cikinta.

“Girman kansu da son mulki ya sake jefa kasar mu a wannan mummunan yanayin, ban da dibar karan mahaukaciya da suke yi wa tsarin shugabanci da ya haifar mana da matsalar tsaro,” inji Kwankwaso.

Ya kuma ce jagororin sun yi wa tattalin arzikin Najeriya kamshin mutuwa, wanda ya haifar da rashin aikin yin da ya yi katutu a kasar.

Kazalika, Kwankwaso ya koka kan mutuwar ilimi musamman ma a makarantun gaba da Sakandare a Najeriya, wanda ya alkawarta ba shi muhimmanci da zarar ya dare karagar shugabancin a 2023.

A nasa bangaren, Mataimakinsa a takarar, Bishop Idahosa, ya amince da fitowa a takarar a 2023, tare da bayyana cewa Najeriya na bukatar sabon hannun da zai kwato ta daga yanayin da take ciki.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi kokarin karbar katin zabensu na dindindin domin samar da sauyin da suke muradi.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Alhamis ce NNPP ta bayyana Bishop din a matsayin dan takararta na Mataimakin Shugaban Kasa a zaben 2023.