✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta lashi takobin raba titunan jihar da mabarata da ’yan talla

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na raba titunan jihar daga masu gararanba da sunan bara ko talla.

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na raba titunan jihar daga masu gararanba da sunan bara ko talla.

Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar, Dakta Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan lokacin da take zantawa da ’yan jarida a ofishinta a Kano ranar Litinin.

Ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa wurin ganin an sami nasarar aiwatar da shirin, musamman kan wadanda suke gararanbar ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Kwamishiniyar ta ce Gwamnatin Jihar ta tattauna da masu ruwa da tsaki a fadin jihar, ciki har da shugabannin al’umma da na addini daga masarautun jihar guda biyar domin lalubo bakin zaren matsalar.

Dakta Zahra’u ta kuma ce jihar ta fitar da kudi Naira miliyan hudu domin fara aikin ka’in da na’in.

Kazalika, Kwamishiniyar ta ce a kwanan nan ma’aikatarta ta karbi wasu rukunin almajirai biyu da aka dawo da su Kano daga jihar Kaduna.

Ta kuma ce nan ba da jinawa ba za a tsugunar da wasu mutane 47 maza da mata dake gararanba a kan tituna domin gyaran hali sannan a raba su da titunan.